Karin kudin wuta ya zama dole — NERC

Wutar lantarki a Najeriya Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Wutar lantarki a Najeriya

A Najeriya hukumar da ke sa ido kan harkar samar da wutar lantarki NERC, ta yi karin haske game da dalilan da suka janyo kara kudin wutar lantarki a kasar.

A wata hira da BBC mataimakin Janar Manaja mai kula da kayyade farashin wutar lantarki a Hukumar ta NERC, ya ce kudaden da hukumar ke samu ba za su isa a rika biyan kamfanonin da ke da ruwa da tsaki wajen samar da wutar lantarki ba.

Abdulkadir Shettima ya ce don haka karin ya zama dole idan ba haka ba babu yadda za a yi a samu gyara hanyoyin bayar da wutar lantarkin ba.

A ranar Litinin ne dai kungiyar kwadagon kasar ta gudanar da wata zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin kudin wuta da aka yi a kasar da kashi 45.

Hukumar dai ta nanata cewa karin kudin wutar shi ne mafi alkhairi, saboda samun ci gaban da ake bukata wajen inganta wutar lantarki a kasar.

A bisa yarjejeniyar da kamfanonin samar da wutar lantarkin da kuma gwamnatin Najeriyar da suka rattabawa cewa nan da shekara ta 2018 ne za a kara ingancin wutar lantarkin tare da kuma rage farashin.