An yi zanga-zanga kan kudin lantarki a Najeriya

Image caption Kungiyar kwadagon ta ce har yanzu akasarin 'yan Najeriya ba sa samun wutar lantarki.

Kungiyar kwadago ta Najeriya,NLC ta gudanar da zanga-zanga a duk fadin kasar domin nuna kin amincewa da karin kudin wutar lantarki a kasar.

Kungiyar, wacce ke yin zanga-zangar tare da wasu kungiyoyi masu zaman kansu da na kare hakkin dan adam, ta ce bai kamata hukumar da ke sa ido kan wutar lantarki ta kara kudin wutar ba.

A makon jiya ne dai hukumar da ke sa ido kan wutar lantarkin ta kara kashi arba'in cikin dari na kudin wutar lantarkin, tana mai cewa ba za ta iya ci gaba da bayar da wutar lantarkin kan farashin na baya ba.

Sai dai kungiyar kwadagon ta ce har yanzu fiye da rabin 'yan kasar ba sa samun hasken wutar lantarkin, don haka ba ta ga dalilin kara kudin wutar ba.

Tun a lokacin gwamnatin marigari Shugaba Umaru Musa 'Yar Adua ne dai, gwamnatin kasar ta ce za ta rika kara kudin wutar a hankali har ta janye hannu a harkar, domin bunkasa samar da hasken wutar lantarki a kasar.