An dakile fashi a jirgin ruwa a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP Vietnam Coast Guard
Image caption Fashi a jiragen ruwa ya zama ruwan dare a Najeriya

Rundunar Sojin ruwan Najeriya ta dakile wani hari da 'yan fashi a teku suka yi yunkurin yi a wani jirgin ruwa na daukar kaya a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur.

Mai tuka jirgin, wadda mace ce 'yar kasar Afrika ta kudu, ta hana su shiga dakin injin jirgin kafin a kai masu dauki.

Jirgin daukar kayan mai suna Safmarine Kuramo na kasar Singapore ya taso ne daga kasar Congo zuwa garin Fatakwal a kudancin Najeriya.

Kaptin din jirgin da sauran ma'aikatan jirgin su ashirin da hudu sun kulle kansu a cikin dakin da injin jirgin ya ke, kuma duk da harbe-harben da 'yan bindigar suka rinka yi domin su bude ba su bude ba, har sai da aka kawo musu dauki.

Fashi a jiragen ruwa da kuma garkuwa da ma'aikatan jiragen ya zamo ruwan dare a yankin Naija Delta mai albarkatun man fetur a Najeriya.