Turkiyya za ta cigaba da taimakawa 'yan gudun Hijrar Syria

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan gudun hijrar Syria

Yayinda dakarun gwamnatin Syria ke cigaba da kai hare-hare a kusa da birnin Aleppo, kasar Turkiyya ta ce babban abin da ya dame ta shi ne samar da tallafi a cikin Syria domin wadanda suka bar gidajensu sakamakon rikicin kasar.

Mataimakin Firaminista Turkiyya, Numan Kurtulmus ya ce yanzu haka kasarsu na bawa 'yan kasar Syria da ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijra daban-daban da ke kusa da iyakar su kusan dubu saba'in da bakwai.

Numan Kurtulmus ya yi gargadin cewa adadin su zai iya karuwa.

Tunda farko shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce irin mawuyacin halin da fararen hula su ka shiga sakamakon hare-haren da Rasha ke kaiwa na bama-bamai, na matukar bata tsoro.