Mahara sun kashe dan majalisa a Ghana

Hakkin mallakar hoto Ghana parliament
Image caption Margayi Joseph Boakye Danqua Adu ya rasu yana da shekaru 51

'Yan sanda a Ghana sun ce an kashe wani dan majalisar dokoki Joseph Boakye Danqua Adu, inda aka daba masa wuka a gidanda da ke birnin Accra.

Babu cikakkun bayanai kan yadda lamarin ya auku, amma 'yan uwansa sun ce maharan sun haura katanga ne da tsani sannan suka shiga cikin dakin kwanciyarsa.

Wannan ne karon farko da aka kashe dan majalisar dokoki a kasar a Ghana.

Galibin 'yan majalisar dokoki a Ghana ba sa samun kariya daga 'yan sanda sai da masu rike da mukaman shugabanci a majalisar.