Shugaban kamfanin Google ya fi kowa karbar kudi a Amurka

Shugaban kamfanin Google Sundar Pichai ya fi kowa karbar kudi

Asalin hoton,

Bayanan hoto,

Shugaban kamfanin Google Sundar Pichai ya fi kowa karbar kudi

An bawa shugaban kamfanin Google Mr Sundar Pichai hannun jarin da ya kai na dala miliyan 199.

Wannan dai ya bashi damar kasancewa shi yafi kowa karbar kudi a shugabannin kamfanoni na Amurka.

Mr Pichai ya zamo shugaban kamfanin ne bayan da a ka kirkiro uwar kamfanin mai suna Alphabet.

Wadanda suka kirkiro kamfanin na Google Larry Page da Sergey Brin sun tara arzikin da ya kai dala biliyan 34.6 da kuma dala biliyan 33.9, kamar yadda mujallar da ke bayyana attajiran duniya ta Forbes ta wallafa.

Wannan kyautar hannun jarin da aka bawa Mr Pichai ta sanya hannun jarinsa ya karu ina ya kai dala miliyan 650.

Za a rinka bawa mr Pichaiikon mallakar hannun jarin a dukkan wattani uku na shekara har zuwa shekarar 2019.