IS ka iya hadewa da Boko Haram - MDD

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mayakan IS a Libya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a kullum kungiyar da ke ikirarin kafa daular Musulunci ta IS tana kara fadada wuraren da ke karkashin ikonta a Libya.

Wakili na musamman na Majalisar, Martin Kobler ya ce hadarin da ke tattare da hakan shi ne kungiyar ka iya kara karfi a Afrika ta yadda za ta hade da kungiyar Boko Haram a Nijar da Chadi da Najeriya.

Mista Kobler ya shaida wa BBC cewa masu tayar da kayar bayan suna amfani da rashin gwamnati a Libya wajen kara karfi.

Don haka ne ya yi kira da a samar da gwamnatin hadin gwiwa nan ba da dadewa ba, a kasar ta Libya.

Tun bayan hambarar da gwamnatin gaddafi an samu rarrabuwar kawuna ta fuskar siyasa da kabilanci a Libya.

A shekarar 2011 ne dai aka kawo karshen mulkin marigayi Mu'ammar Gaddafi a Libya