Kano: Gobara ta tashi a kasuwar Kurmi

Hakkin mallakar hoto Myanmar Fire Service
Image caption Gobara ta tashi a kasuwar Kurmi

Rahotanni daga birnin Kano da ke arewacin Najeriya na cewa gobara ta tashi a kasuwar Kurmi mai dadadden tarihi.

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe takwas na daren ranar Talata.

Wani ganau wanda yake kuma da shago a kasuwar, Auwalu Skido Mai riguna, ya shaida wa BBC cewa shaguna biyu ne na kayan doki suka kone.

Mutumin ya ce bayan da suka ga wutar na ci a shagunan saboda gudun kada ta kama sauran shaguna, sai suka kira jami'an kashe gobara, kuma ba da jimawa ba suka zo suka kashe wutar.

Ya kuma kara da cewa akalla kayan da suka kone a shagunan sun kai na naira miliyan uku.

Ba a dai samu asarar rai ko daya a gobarar ba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da gobara ta tashi a kasuwar ba.