Trump da Sanders sun yi nasara a New Hampshire

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An zabi mutanen biyu ne domin mutane sun gaji da halayen 'yan siyasar asali.

Mai son yin takarar shugabancin kasa na jam'iyar Republican a Amurka, Donald Trump, da takwaransa na Democrat, Bernie Sanders sun yi nasara a zaben fitar da gwanin da aka gudanar a jihar New Hampshire.

Da alama Mista Trump zai ninka kuri'un da wanda ya zo na biyu a zaben, gwamnan jihar Ohio, John Kasich, zai samu.

Gwamnan jihar Florida Jeb Bush da gwamnan jihar Texas, Sanata Ted Cruz da dan majalisar dattawa da ke wakiltar Florida Marco Rubio ke a matsayi na uku.

Mista Trump ya shaida wa magoya bayansa cewa yana son Amurka ta kara samun tagomashi a kasashen duniya.

A bangaren jam'iyar Democrat, Mista Sanders, wanda ya doke Hillary Clinton da tazara mai yawa, ya ce shi da magoya bayansa sun aike da sakonnin cewa gwamnati ta kowa ce, ba wai ta wasu daidaikun attajirai masu bayar da gudumawa a yakin neman zabe ba.

A cewar sa, zaben nasa ya nuna cewa mutane suna son a samu "sauyi na hakika" a kasar.

Ita kuwa babbar mai hamayya da shi, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce za ta ci gaba da yin fafitikar neman kuri'u a yakin neman zaben.