Nigeria ta kama sojoji masu sayar da makamai

Image caption Sojin Najeriya sun kama makamai

Rundunar sojin Nigeria ta ce ta kama wasu sojojinta da ake zargi da yunkurin sayar da makamai ga 'yan kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar, Kanal Sani Usman Kuka Sheka, ya shaida wa manema labarai cewa a ranar Lahadin da ta gabata ne aka kama biyu daga cikinsu a tashar mota ta Yola da wasu makamai da albarusai na soja suna neman kai wa wasu wurare.

Ya ce suna amfani da wata dama ta bude kasuwanni da aka yi a Borno da Yobe suna hada baki da 'yan ta'adda suna sayar musu da makamai.

An kuma same su da gurneti mai hayaki, harsasai dubu biyu da dari da talatin da shida, da wasu harsasai na musamman guda hamsin, da kuma harsasai na bindigodi masu sarrafa kansu.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike kuma nan bada jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotun soji bisa zargin da ake musu.