Boko Haram ta fito da sabbin hanyoyin kai hare-hare

Image caption Dubban mutane ne ke ci gaba da zama a sansanonin 'yan gudun hijirar Najeriya.

Ministan tsaron Najeriya ya shaida wa BBC cewa mayakan kungiyar Boko Haram suna yin bad-da-kama, inda suke tayar da bama-bamai a sansanonin 'yan gudun hijira.

Birgediya Janar Muhammad Mansur Dan Ali [Mai ritaya] ya ce labaran da ya samu sun nuna cewa a makon jiya da kuma ranar Litinin 'yan Boko Haram sun shiga sansanonin 'yan gudun hijira domin su tayar da bama bamai.

A cewarsa, "Wannan wani sabon salo ne da 'yan kungiyar suka fito da shi saboda sun ga an fi karfinsu a filin-daga, sun dawo cikin jama'a suna barna."

Ya ce suna so su mayar da mutanen gidajensu domin rage yiwuwar kai musu hare-hare.

Sai dai ministan ya soma ne da bayyana halin da 'yan gudun hijirar ke ciki:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Da ma dai 'yan gudun hijira da dama sun dade suna kokawa da rashin tsaro a sansanonin su.