Gwamnatin Syria zata kwato birnin Aleppo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwamnatin Syria zata kwato birnin Aleppo

Wata ta hannun daman shugaban kasar Syria Bashar al-Assad, ta bayyana cewa dakaru masu goyon bayan gwamnati sun yi aniyar cigaba da kai farmaki a arewacin kasar har ya zuwa kan iyakar kasar Turkiyya.

Bouthaina Shaaban ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa gwamnati da aminanta za su kuma yi kokarin sake kwato birnin Aleppo.

Ta kuma yi watsi da kiraye-kirayen tsagaita wuta da kungiyoyin 'yan tawaye suka nema a matsayin wani sharadi da zai sa su halarci taron tattaunawar sulhun da MDD ke marawa baya.

Kungiyoyi masu bada agajin jin kai sun sake yin kiran da suke yiwa kasar Turkiyya da ta bar dubban mutanen da suka tsere daga tashin hankalin su shiga kasarta.

Majalisar dinkin duniya ta kididdige cewa fadan da ake yi zai hana kai kayan agaji ga mutane dubu dari uku dake birnin n Aleppo.