Zuma na fuskantar tuhuma kan gyaran gida

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wani rahoto mai zaman kansa da aka fitar a 2014 ya ce Zuma ya amfana da kudaden ba bisa ka'ida ba

An fara shari'ar da 'yan adawa suka shigar da shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma, a kotu kan gyaran gidansa na kashin kansa.

'Yan adawar dai suna so Zuma ya biya kusan dala 23 miliyan da aka kashe wajen gyaran gidansa na kauyen Nkandla.

Mista Zuma dai ya yi tayin biyan wasu daga cikin kudaden, sai dai ana ci gaba da shari'ar.

Masu goyon bayan shugaba Zuma da kuma babban abokin adawarsa Julius Malema suna yin zanga-zanga a Johannesburg.

Mai magana da yawun kungiyar da ke ikirarin yaki da yi wa tattalin arziki ta'annati ta EFF ya ce bore na nuna adawa ne ga "Cin ahnci da rashawa da kuma nada 'yan uwansa kan mukamai ba bisa ka'ida ba".

Jam'iyyar ANC ta kira zanga-zangar da aka yi zuwa kotu da cewa siyasa ce.