Boko Haram ta sake kai hari a Kamaru

Image caption A baya bayan nan dai Boko Haram ta matsa kaimi wajen kai hare-hare a kasar ta Kamaru.

Wasu 'yan kunar-bakin-wake da ake zargi 'yan Boko Haram ne sun kai hari a wani kauye da ke arewacin Kamaru, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 11.

Rahotanni na cewa 'yan kunar-bakin-wake biyu da suka kai harin a kauyen Nguetchewe da ke kusa da kan iyaka da Najeriya, na cikin mutanen da suka mutu.

Haka kuma mutane ashirin sun jikkata.

A 'yan kwanakin nan dai 'yan kungiyar ta Boko Haram sun matsa kaimi wajen kai hare-hare a kasar ta Kamaru.

Kasar dai na cikin kasashen da suka yi gamayya domin murkushe kungiyar.