An kashe mutum 56 a sansanin Dikwa

Akalla mutane 56 ne suka rasu, a yayin da wasu kusan 66 suka samu raunuka sakamakon harin kunar bakin wake a sansanin 'yan gudun hijira da ke Dikwa a jihar Bornon Najeriya.

Shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Borno, Injiniya Satomi Alhaji Ahmed, ya shaida wa BBC cewa 'yan kunar bakin wake uku ne suka tayar da bama-bamai a lokacin da 'yan gudun hijirar ke layin karbar abincin safe:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Lamarin ya auku ne a ranar Talata amma kuma sai a ranar Laraba aka soma samun bayanai game da harin.

A cewarsa, jami'an tsaro sun kama daya daga cikin 'yan kunar bakin waken, wacce ta ki tayar da bam din da yake jikinta saboda iyayenta suna cikin sansanin.

Ya kara da cewa akwai jami'an tsaro a sansanin lokacin da aka kai harin, yana mai cewa yawan 'yan gudun hijirar da ke wurin ne ya sa ba a iya gano masu niyyar yin kai hare-hare da wuri.

Injiniya Satomi Alhaji Ahmed yace 'yan gudun hijira sama da dubu hamsin ne ke samun mafaka a sansanin na Dikwa.

Jami'an aikin agaji na jihar Borno wadanda suka tabbatar wa BBC adadin sun ce an tsaurara tsaro a sansanin wanda ke da mutane 50,000.