Amurka ta yi Allah-wadai da harin Dikwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Miliyoyin mutane sun rasa muhallansu a Borno

Gwamnatin Amurka ta yi Allah-wadai da harin kunar bakin wake da aka kai a sansanin 'yan gudun hijira da ke Dikwa a jihar Borno.

A sakonta na jaje, Amurka ta ce za ta ci gaba da taimakon wadanda suka rasa muhallansa a arewa maso gabas ta hanyar bayar da kayayyakin jin kai.

Amurkar ta kuma jaddada goyon bayanta ga Najeriya a yaki da ta'addanci.

Akalla mutane 56 ne suka rasu a yayin da wasu kusan 70 suka jikkata sakamakon harin kumar bakin wake a sansanin na Dikwa a ranar Talata.

Tuni gwamnatin Najeriya ta umarci jami'an tsaron kasar da su kara tsaurara matakan tsaro a sansanonin 'yan gudun hijira da ke sassa daban-daban na kasar.

Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya bayar da umarnin, ya kuma nuna alhini game da hallaka 'yan gudun hijira a harin da wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake suka kai a sansanin su da ke garin Dikwa na jihar Borno.