Ana cikin mawuyacin hali a Aleppo

Image caption Mutane na cikin mawuyacin hali a Aleppo

Kungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa mawuyacin halin da jama'a ke ciki a Syria sakamakon rikicin da ake a birnin Aleppo, ya na nema ya zamo wani babban bala'i.

Kungiyar agaji ta Red Cross ICRC ta ce makonni biyu kenan babu ruwan sha a birnin, sannan duk an lalata ma'adinan ruwan.

Wasu daga cikin hanyoyin da ake bi ana kai kayan agaji birnin yanzu ba sa biyuwa, kuma ana fama da karancin man fetir da kuma hasken wutar lantarki.

Kungiyar likitocin sa kai ta Doctors Without Borders ta ce hare-hare ta saman da ake kai wa sun shafi asibitoci uku da suke aiki a ciki.

Kusan mutane dubu hamsin ne suka tsere daga birnin saboda fadan da ake gwabzawa wanda Rasha ke marawa dakarun gwamnatin Syria baya.

Kungiyar agajin ta Red Cross din ta ce akwai bukatar kai daukin abinci da ruwa da kuma magunguna a birnin na Aleppo.