An soma shari'ar 'yan Shi'a a gidan yari

'Yan Shi'a na son a saki shugabansu, Sheikh El-Zakzaky
Bayanan hoto,

'Yan Shi'a na son a saki shugabansu, Sheikh El-Zakzaky

A jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, an soma shari'ar wasu 'yan kungiyar Shi'a da ake zargi da hannu a rikici a tsakanin 'yan kungiyar da sojoji a Zariya.

'Yan Shi'a kusan 200 aka gabatar ga kotun da ta zauna a cikin gidan yarin Kaduna domin tsaro.

An dai bayar da belin mutane hudu daga cikin wadanda ake zargin.

A cikin watan Disambar bara, aka yi tashin hankali tsakanin 'yan Shi'a da sojojin Najeriya, lamarin da ya janyo rasuwar mutane da dama tare da tsare shugaban kungiyar, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Haka kuma tuni gwamna Nasir Ahmed El-Rufai ya rantsar da kwamitin shari'a domin binciko musabbabin rikicin da ya faru a tsakanin sojojin da 'yan mazhabar Shi'a.

Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa kwamitin mai wakilai 13 ne a karkashin jagorancin wani babban alkali na kotun daukaka kara ta tarayya, Mai shari'a Mohammed Lawan Garba.