Nigeria za ta tsaurara tsaro a sansanonin 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto Yusuf Shettima
Image caption Farfesa Osinbajo ya bukaci a kara matakan tsaro a sansanonin 'yan gudun hijira.

Gwamnatin Nijeriya ta umarci jami'an tsaron kasar da su kara tsaurara matakan tsaro a sansanonin 'yan gudun hijira da ke sassa daban-daban na kasar.

Mukaddashin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya bayar da umarnin, ya kuma nuna alhini game da hallaka 'yan gudun hijira a harin da wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake suka kai a sansanin su da ke garin Dikwa na jihar Borno.

Mista Osinbajo ya kuma ce gwamnatin Nijeriya za ta kara kaimi na ganin ta gano tare hukunta duk wadanda ke da hannu wajen hallaka fararen hula da ba su ji ba su gani ba.

A nata bangaren, gwamnatin jihar Borno ta ce tana daukar nauyin kula da mutane da suka jikkata a harin kunar bakin wake a sansanin 'yan gudun hijira da ke garin Dikwa na jihar.