'Assad zai dakatar da bude wuta a Syria'

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Mr Putin shi ne ke mataimakawa Assad da makamai

Babban na hannun daman Rasha, Shugaba Basharul Asad na Syria, ya ce a shirye yake ya tattauna yiwuwar dakatar da wuta a fadan da ake yi a kasar.

Mataimakin Ministan harkokin wajen Rasha, Gennady Gatilov, ya ce za a duba hakan a Munich, inda nan gaba manyan kasashe za su gana don tattauna yadda za a kawo karshen fadan.

Wakilin BBC ya ce "Amurka na cewa Rusha tana neman kara jan jiki ne kawai, tana fata za a ragargaza abokan adawar Basharul Asad kafin duk wani shirin dakatar da wuta ya soma aiki cikin makwannin da ke tafe."

Hare-haren Rasha ta sama dai sun taimaka ma gwamnatin Assad sake kama wurare da dama.