Kotu ta tabbatar da zaben gwamnan Taraba

Image caption Kotun ta ce Darius Ishaku na jam'iyyar PDP shi ne gwamnan jihar Taraba.

Kotun kolin Najeriya ta amince da zaben Darius Ishaku a matsayin Gwamnan Jihar Taraba.

Kotun ta yi watsi da daukaka karar da 'yar takarar jam'iyyar APC, Aisha Alhassan ta yi, tana mai cewar ba shi da tasiri.

Wannan hukunci dai ya tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta zartar tun farko.

Kotun ta ce za ta bayar da dalilanta dangane da hukuncin a ranar 22 ga watan Fabrairu.

Tun bayan zaben da aka gudanar a ranar 11 ga watan Afrilun 2015, Aisha Alhassan ta jam'iyyar APC ta yi zargin an tafka magudi tare da kura-kurai a zaben da aka sanar da Darius Ishaku a matsayin wanda ya yi nasara.

A cikin watan Nuwamba kotun sauraron kararrakin zabe ta yi soke zaben, amma kuma kotun daukaka kara a cikin watan Disamba ta ce zaben halataccen ne.