An yi kokarin sake kwakwale idon wani yaro a Zariya

Hakkin mallakar hoto BBC Nurah Ringim
Image caption Yaron da aka kwakwale wa ido a cikin watan Janairu

Wasu da ake zargin matsafa ne sun yi kokarin kwakwale idon wani yaro a unguwar Banzazzau da ke Zariya a jihar Kaduna, kafin mutane su fatattake su.

Mutanen sun nemi cire idon wani yaro dan shekaru biyu, wanda har sun daure masa hannu, kafin wasu matasa su gansu a ranar Talata.

Kwamandan 'yan sanda a Zariya, ACP Mohammed D. Shehu ya tabbatar wa BBC labarin, inda ya ce tuni suka soma bincike a kan lamarin.

"Na gayyaci mutanen unguwar domin in ji ko za su gane daya daga cikin mutanen da suka yi kokarin cire wa yaron ido, amma dai babu wanda ya iya gane mutanen," in ji Shehu.

Mataimakin kwamishinan 'yan sandan ya kara da cewar "Allah ne ya kubutar da yaron, don mutanen har sun daure masa hannu."

Lamarin na zuwa ne kasa da wata guda bayan da aka kwakwale wa wani yaro dan shekaru uku, idanunsa biyu a cikin unguwar ta Banzazzau.

A yanzu haka dai, yaron yana samun kulawa a asibiti kuma likitoci sun tabbatar da cewa zai kasance makaho.