Areva ta gurbata muhalli a yankin Agadez

Kamfanin Areva da ke Jamhuriyar Nijar
Image caption Katafaren kamfanin mallakar Faransa na aikin hako uranimuim ne a Nijar

A Jamhuriyar Nijar, wasu kungiyoyin farar-hula masu aiki a fannin ma'adanai sun koka game da gurbata muhalli da kamfanin Areva ke yi a yankin jahar Agadas.

Lamarin da suka ce na jefa ma'aikatan kamfanin da sauran al'umomin yankin cikin hadarin kamuwa da cututtuka.

A shekarar 2012 ne kamfanin na Areva ya fitar da wani shirin kyautata lafiyar al'umomin yankin, shirin da kungiyoyin farar hular suka ce yana tafiyar hawainiya.

Shugabar kungiyar Grain Madam Sole Ramatou ta ce kamfanin Areva ba ya kula da mahalli.

Haka kuma yawancin ma'aikatan kamfanin da suka kamu da cututtuka ba a cika fayyace ainihin abin da ke damun su ba har sai ciwo ya ci karfinsu, daga bisani kuma su ce ga garin ku nan.

Ma'aikatan kamfanin sun yi zanga-zanga a shekarun baya domin nuna kin amincewa da rashin kula da lafiyarsu.