Zika ta hallaka matashiya a Brazil

Sauron da ke yada cutar Zika
Image caption Masana sun ce cutar Zika na janyo tawaya a kwakwalwa.

Hukumomin lafiya a Brazil sun ce wata cuta mai alaka da Zika ta yi sanadin mutuwar mata 'yar shekara 20, kuma ita ce ta uku a tsakanin mutanen da suka manyanta da cutar ta halaka daga lokacin da aka sanar da barkewar annobar Zika, watanni tara da suka wuce.

Sai dai Ministan lafiyar kasar bai fito fili ya ce cutar Zikar ce ta kashe matar ba.

Ana dai jibinta annobar ta Zika da larurar tsimburewar kwakwalwar da ta shafi jarirai sama dubu hudu.