An gano torokon maganadisun duniyoyi

Hakkin mallakar hoto LIGO
Image caption Masana kimiya sun ce an samu gagarumin ci gaba

A ci gaban da ake kira mafi muhimmanci cikin fiye da karni guda, masana kimiyya a Amurka sun ce sun yi nasarar gano torokon maganadisun duniyoyi.

Albert Einstein ya yi hasashen cewa akwai wannan toroko tun karni guda a baya, amma sai yanzu aka yi nasara iya ganin su.

Abin da ke kawo shi, shi ne karon bakaken ramuka a sararin sama, su kuma keta sararin, kana su mike, kamar dai yadda Einstein din ya kintata.

Masu binciken suka ce abin da suka ganon yana da burgewa, kuma ya ba da sabuwar hanya ta kallon sararin samaniya.

Hakan kuma zai ba da damar nazari sosai a kan bakaken ramuka da taurarin nutiron - da sauran ma abin da ba mu san akwai su ba.