An mika sojoji 12 ga EFCC a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rundunar sojin ta sallami wasu sojojin 250 da ta samu da aikata ba daidai ba a jihar Kaduna

A Nigeria, rundunar sojin kasar ta ce ta tura Sojoji 12 ga hukumar da yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, domin ta bincike su.

Sojojin da za a tuhuma dai suna bakin aiki ne, wadanda suka hada da, wasu masu mukamin Manjo Janar su uku, daya daga cikinsu ya yi ritaya, da Birgediya Janal uku, da masu mukamin Kanar su hudu, wani Laftanal Kanar daya.

Haka kuma, rundunar sojin ta ce da zarar hukumar EFCC ta kammala nata binciken, za a mika duk wanda aka samu da laifi ga kotun sojojin Nigeria domin yanke masa hukunci daidai da laifin da ya aikata.

Sai dai sanarwar mai da sa hannun mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar sojin ba ta bayyana takamaiman lafukan da suka aikata ba.

Ana zargi wasu sojoji da yin sama da fadi da wasu kudaden da aka ware domin yaki da Boko Haram, haka kuma ana zargin wasu sojojin da karbar na goro a lokacin mayna zabukan da aka yi a shekarar 20115.