'An kama wanda ya janyo fashewar bututan mai a Nigeria'

Image caption An samu kananan jiragen ruwa da jarkoki da tankuna da ake amfani da su wajen satar man da gas

Dakarun Nigeria a yankin Niger Delta sun ce sun kama wanda ake zargin ya yi makarkashiyar fashewar bututan mai na kamfanin mai na Agip a Nigeria.

Harin ya faru ne a watan Janairun daya gabata a jihar Bayelsa kuma ya janyo malalar mai a yankin.

A bayyana kama Yarima Alvin Cockman Oyegun da aka fi sani da kwamanda Abula, a cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar.

A wani labarin kuma rundunar hadin gwiwa ta JTF a yankin, ta ce ta kama wadansu jiragen ruwa biyu dauke da danyen mai da kuma man gas da suka yi zargin cewa na sata ne a yankin Niger Delta mai arzikin mai.

Wata sanarwa da rundunar hadin gwiwa ta JTF ta fitar dauke da sa hannun kakakinta, Isa Ado, ta ce ana gudanar da bincike a kan jirgin "African Sky" da ke dauke da tan 670 na danyen mai na sata.

An kuma kama wani jirgin ruwan mai suna "Eucharia 111" dauke da man gas, wanda aka ajiye a kusa da wani wuri da ake satar mai.

Haka kuma sanarwar ta kara da cewa dakarun Najeriyar sun lalata wadansu wuraren da ake satar danyen mai da man gas a jihohin Bayelsa da kuma Delta duka a yankin na Niger Delta.

A cewar JTF, sojoji sun kama wadansu mutane bakwai da suke zargi da hannu a satar danyen man da gas da kuma ayyukan fashin teku.

Najeriya dai na asarar biliyoyin naira ta hanyar satar danyen mai.