An tsige Nyako ba bisa ka'ida ba - Kotu

Wata kotun daukaka kara a jihar Adamawa da ke Najeriya, ta yanke hukuncin cewa ba a bi ka'ida ba wajen tsige tsohon gwamnan jihar Murtala Nyako.

Hukuncin da mai shari'a Tunde Ayotoye ya jagoranta ya bayyana cewa ba a bai wa Nyako damar kare kansa ba, a lokacin da aka dauki matakin tsige shi.

Kotun wadda ke zamanta a birnin Yola ta kara da cewa, yin hakan ya keta hakkin Nyako, saboda haka ta soke tsige shi da aka yi.

A watan Julin shekarar 2014 ne dai aka tsige Nyako daga gwamna, bayan majalisar dokokin jihar ta amince da wani rahoton kwamitin bincikensa kan zargin cin hanci da rashawa.

Kotun dai ta umarci a biya tsohon gwamnan dukkan hakkokinsa.