'Yan mata masu ciki na karuwa a Afrika ta Kudu

A kasar Afrika ta Kudu yawan 'yan matan da ke yin ciki na karuwa, inda aka yi kiyasin cewa mata dari uku ne ke daukar ciki a kullum.

Hakan na faruwa ne a kasar da ake koya wa 'yan makaranta mu'amala tsakanin 'yan mata da samari.

Kuma a kasar da ake bayar da kulawa kyauta ga mata masu juna biyu.

Sai dai a wani yukuri na magance matsalar, wata gwamnan tsakiyar uThukela ta ce za ta dauki nauyin karatun duk wata yarinyar da bata taba sanin da namiji ba.

Dudu Mazibuko ta ce tana sa ran hakan zai karfafawa 'yan mata gwiwar maida hankali a kan karatunsu....a maimakon su zama iyaye.

Ta ce "Daukar nuyin karatun ba wani lada ba ne muke bayarwa ba, tamkar jari ne muke zubawa a rayuwar 'yan matan. Kuma mu ba ma kushewa wasu da ba su kare budurcinsu ba, domin su ma 'ya'yanmu ne."

Sai dai za a rika yi wa 'yan matan gwaji akai-akai, domin tabbatar da budurcinsu kafin a cigaba da daukar nauyin karatunsu.

Thubelihle Dlodo na daga cikin 'yan mata 16 da ke cin gayiyar wannan shiri.

Ta yi karin bayani kan matakin da ta dauka "Na yanke shawarar tsare mutuncina ne saboda bana son in kamu da cututtuka daga wani namiji. Ina fatan wasu 'yan matan za su amfana daga dabi'unnmu saboda su cimma burinsu a rayuwa."

Sai dai wasu na ganin gwajin tabbatar da budurcin 'yan matan, tamkar shishshigi ake yi musu; suna masu cewa neman ilmi wani abu ne daban da bai shafi harkar soyayya ba.

Image caption Daliban da suka kare budurcinsu za su yi rawa a wani bikin al'ada na 'yan mata

Wata mai rajin kare mata daga cin zarafi, Palesa Mpapa na da wannan ra'ayi:

"Wannan mataki tamkar nuna banbanci ne, kuma ba zai magance yaduwar cutar HIV ko Sida ba; sannan yawan daukar cikin da 'yan mata ke yi, bai kamata a dora laifi a kansu kawai ba."

Wannan tsarin dai ya haddasa mahawara da kuma tayar da jijiyoyin wuya a kasar.

Amma ana sa ran zai sa 'yan mata daukar matakan da suka dace wajen tsare mutuncinsu.