Zan kwato dukkan yankunan Syria - Assad

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Assad na samun taimako daga Putin

Shugaban Syria, Bashar al-Assad, ya ce yana shirin ci gaba da yaki, har sai ya kwato dukkan yankunan kasar sun koma karkashin ikonsa.

A hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Faransa, ya ce "Zai dauki lokaci mai tsawo" kafin ya samu galaba a kan masu hamayya da shi.

Assad ya kara da cewa zai ci gaba da yaki da wadanda ya kira 'yan ta'adda har a lokacin da ake tattaunawar zaman lafiya.

An shafe watanni masu yawa da ke nuna rashin karfin dakarun Shugaba Assad.

Amma saboda tallafin Rasha na jiragen yakin sama, a yanzu dakarun Syria na samun galaba.