An sako mutane 275 da aka zarga da Boko Haram

Image caption Wadanda ake tuhuma da zama 'yan boko haram

Rundunar sojin Najeriya ta mika mutane 275 ga gwamnatin jihar Borno, wadanda aka kama tun farko bisa zarginsu da kasancewa 'yan Boko Haram.

An mika wa gwamna Kashim Shettima mutanen ne bayan da sojoji suka tantance su, aka tabbatar basu da hannu a ayyukan ta'addanci.

Kakakin gwamnan Borno, Malam Usman Kumo ya shaida wa BBC cewa daga cikin wadanda aka sako har da "maza 142 da mata 49 da kuma kananan yara maza da mata su 77".

Kumo ya kara da cewa " A yanzu an kai mutanen wurin koyan sana'o'i, daga bisani za a basu jari domin dogaro da kansu bayan sun kammala koyon sana'ar."

Gwamnatin jihar Borno ta kuma ce kananan yaran za a saka su a makaranta domin su samu ingantacciyar rayuwa.

A cikin watan Satumbar bara ma, sai da rundunar sojin kasar ta sako wasu mutane 128 inda ta mika su ga gwamnatin jihar Borno bayan ta tabbatar basu da alaka da kungiyar Boko Haram.