An kai hari kauyen Shuwari a jihar Borno

Image caption Sojojin Najeriya sun yi ikirarin cin karfin kungiyar Boko Haram

A Najeriya wasu mahara da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kauyen Shuwari da bashi da nisa da birnin Maiduguri a jihar Borno.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Borno, Injiniya Satomi Ahmed ya tabbatar wa da BBC aukuwar al'amarin.

Maharan sun kuma kona gidaje kimanin 21 a yayin harin da suka kai a ranar Alhamis da daddare a kauyen.

Wani mutum wanda kauyen su ba shi da nisa da inda lamarin ya auku, ya shaida wa BBC cewa maharan sun je garin ne a kan babura da kuma wata mota guda.

A baya-bayan nan ne 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kai wani mummunan hari a garin Dalori, inda suka kashe fiye da mutane 60.

Kungiyar ta Boko haram dai har yanzu tana rike da wasu kananan hukumomi biyu a jihar Bornon a Najeriya.