Danqua: 'Yan sanda sun yi kame a Ghana

Hakkin mallakar hoto Ghana parliament
Image caption An kashe margayi Danqua a gidansa

'Yan sanda a birnin Accra na kasar Ghana sun ce sun cafke wani mutumi da suke zargi da kashe wani dan majalisan dokokin kasar wato Joseph Boakye Danqua Adu.

An kama mutumin mai suna Daniel Asiedu mai shekaru ashirin da haihuwa ne bisa zargin kashe dan majalisar.

A ranar Talatar da ta wuce ne aka yi wa Mr Danqua kisan gilla a cikin gidansa.

'Yan sandan suka ce mutumin ya shaida musu cewa wasu ne suka sa shi aikata kisan da alkawarin biyansa ladar kudi cedi dubu biyu, kuma ya kashe dan majalisar ne ta hanyar daba masa wuka.

Wannan ne karon farko da aka kashe dan majalisar dokoki a kasar a Ghana.

Galibin 'yan majalisar dokoki a Ghana ba sa samun kariya daga 'yan sanda sai da masu rike da mukaman shugabanci a majalisar.