William Ruto ya yi nasara a kotun ICC

Image caption Hakan na nufin ba za a amince da duk wasu shaidu da masu gabatar da kara suka tattaro kan Ruto ba.

Alkalan kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya, ICC da ke yin shari'a kan mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto sun daina amincewa da "shaidun da suka janye hujjojin da suka bayar" a baya.

Hakan na nufin ba za a amince da duk wasu shaidu da masu gabatar da kara suka tattaro ba , sannan suka gabatarwa kotun a kan zarge-zargen da ake yi masa ba.

Manyan shaidu a kan karar sun sauya shaidar da suka gabatarwa kotun, ko da ya ke masu shigar da kara sun yi zargin cewa sun yi hakan ne bayan an basu cin hanci.

Mr Ruto, wanda ake tuhumarsa da iza wutar rikicin da aka yi bayan zaben shugaban kasar na shekarar 2007, ya musanta cewa ya aikata laifukan take hakkin dan adam.

Rikicin ya yi sandiyar mutuwar akalla mutum 1200.