Zamfara: 'Yan gudun hijra na kukan rashin abinci da matsugunni.

Image caption 'Yan gudun hijrar Zamfara na cikin mawuyacin hali

A jihar Zamfara ta Najeriya daruruwan iyalai ne yawanci mata da yara ne ke fuskantar rashin abinci da matsugunai bayan da suka arce daga kauyukansu domin guje wa hare-haren 'yan fashin shanu.

Rahotannin sun ce yanzu haka dubban mutane sun kwarara cikin garin Dangulbi domin tsira da rayukansu bayan da aka girke jami'an tsaro a garin.

Ko a daren ranar Alhamis an hallaka mutane 18 a wasu kauyuka da ke yankin.

Mazauna garin dai sun ce halin da suke ciki a yanzu ya tsananta, saboda tun bayan da aka kai hari a wancan makon da ya gabata, kusan kullum sai an kai hari wasu kauyukan yankin.

Wani mazaunin Dangulbi da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa mutanen da suke kwarara garin yawancin mata ne da kananan yara, wadanda aka kashe musu mazaje da iyaye.

Mutumin ya ci gaba da cewa, saboda cikar da garin ya yi, da yawa daga cikin mutanen da suka shiga ba su da wajen kwana, ta kai har wasu ma a kasuwa suke kwana.