Za a halalta farautar Dawisu a Indiya

Hakkin mallakar hoto PTI
Image caption Dawisun Indiya

Gwamnatin jihar Goa da ke yammacin Indiya ta ce za ta sanya Dawisu a sahun dabbobin da ke cutar da al'uma a kasar, duk kuwa da cewa Dawisu na daga cikin tsuntsayen alfarma a kasar.

Kuma wannan matakin zai ba da damar farautarsu da nufin rage yawansu.

Minsitan aikin ganar jihar, Ramesh Tawadkar ya ce Dawisun na bata amfanin gona.

A karkashin shirin, baya ga Dawisu za a ayyana Birrai, da Aladen daji da kuma Bauna a matsayin masu hadari, wadanda su ma za a iya farautarsu.

An dai kafa kwamiti na musamman don nazarin tasirin daukan matakin a kan jinsin wadannan halittun.

A kasar Indiya dai ana karrama Dawisu a matsayin dabbar alfarma da ake jibinta ta da sarauta, ana kuma rubuce-rubucen adabi da wakoki a kan ta.

A halin da ake ciki dai dokar kasar ta haramta farautar Dawisu, kuma kungiyoyin kare hakkin dambobi na adawa da shirin da gwamnati ke yi na ayyana shi a sahun tsuntsaye masu cutarwa.