'Yan Najeriya na tuna Janar Murtala

Ana gudanar da bukukuwan tunawa da tsohon shugaban kasar Najeriya, Marigayi Janar Murtala Ramat Muhammad.

A ranar 13 ga watan Augusta 1976, aka kashe marigayin, a wani yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Ana dai yin bikin tunawa da Murtala Muhammad ne sakamakon gudunmuwar da ya bayar wajen gina Nijeriya, musanman ta fukar yaki da cin hanci.

Yau kimanin shekaru arba'in ke nan da wasu dakarun Soja karkashin Buka Suka Dimka suka harbe tsohon Shugaban Najeriyar a lokacin mulkin Soja a wani yunkurin juyin mulkin da bai samu nasara ba.

Marigayi Murtala Muhammad ya kafa tarihi sosai a lokacin mulkinsa musamman kawo dai-daito a tsakanin shugabanni da talakawa, da da'a da biyayya da kuma daraja dukiyar gwamnati.

Marigayin ya kuma kafa tubalin yaki da cin hanci da rashawa a lokacin mulkinsa, sannan ya kirkiro jihohi bakwai a 1976 da kuma samar da safiyon da ya samar da birnin tarayya Abuja.

Janar Murtala Muhammad ya bar duniya yana da kimanin shekaru 37 da haihuwa, an kuma yi jana'izar sa tare da binne shi a mahaifarsa da ke Kano.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti