Rwanda za ta kori 'yan gudun hijirar Burundi

Image caption Burundi ta zargi Rwanda da horas da 'yan gudun hijirar domin su yake ta.

Gwamnatin kasar Rwanda ta ce tana shirin fitar da 'yan gudun hijirar Burundi daga kasar, kwanaki kadan bayan an zarge ta yunkurin tayar da hankali a Burundin.

Gwamnatin ta ce tana shirin fitar da 'yan gudun hijirar na Burundi kimanin 70,000 nan take.

Ana zargin Rwanda da horas da 'yan gudun hijirar da kuma basu makamai domin su rika yaki da gwamnatin Burundin.

Sai dai kasar ta Rwanda ta musanta zargin.

Rikicin kasar ta Burundi dai sai karuwa yake yi tun a watan Afrilu bayan Shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na uku.