Zuckerberg ya fada wasi-wasi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mark Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Mai kamfanin sa da zumunta na facebook, Mark Zuckerberg ya gaggauta kafa katangar karfe tsakaninsa da wani mamba a kwamitin gudanarwar kamfanin, Marc Andreessen wanda kuma ke da tasirin gaske.

Yana dai kokari ne ya takaita illar wani furuci da mamban ya wallafa a shafin twitter, wanda ka iya yi wa Zuckerberg mummunar barana a daidai lokacin da yake kokarin fadada kasuwar facebook a duniya.

Marc Andreessen dai ya yi watsi da matakin da Indiya ta dauka na rufe shirin facebook na samar da intanet da ake samu kyauta ta wayar salula da cewar wani yunkuri ne na mulkin mallaka.

Kuma daga nan sai ya kara cusa wa mutane fargaba dangane da amannar da wasu suka yi cewa Zuckerberg na rabewa da aniyarsa ta tallafa wa al'uma ne wajen mamaye duniyar intanet a kasashe masu tasowa.

Mark Zuckerberg ya ce "wannan furucin na matukar daga mini hankali, kuma bai dace da manufata ko ta facebook ba."

Amma daga bisani Marc Andreessen ya nemi gafara, kana ya goge abin da ya wallafa a shafin nasa na twitter.

Wannan furuci dai yana da illa saboda ya shafi batun yarda, wadda ita ce ginshiki a harkar facebook.