'Boko Haram na samun horo a Somalia'

Hakkin mallakar hoto Screen Grab
Image caption Kungiyar Boko Haram ta yi mubayi'a ga mayakan IS da ke Syria da Iraq.

'Yan Boko Haram na samun horo a Somaliya a cewar shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud.

Shugaban ya fadi haka ne a wani taro a kan tsaro da a ke yi a Munich ta kasar Jamus a ranar Lahadi.

Shugaba Hassan ya kara da cewa 'yan Boko Haram na samun horon soji a kasarsa da ke Gabashin Afrika a bakin teku, sannan su koma Najeriya a yammancin Africa.

Sannan ya kara da cewa 'yan ta'adda na da alaka da juna, kuma kan su a hade yake, kuma su na da tsari, don haka akwai bukatar kasashe su ma su hada kai.

Abinda bai fito karakara ba a jawabin nasa shine ko Al Shabaab har yanzu na horas da 'yan Boko Haram duk da mubayi'ar da kungiyar ta yi wa mayakan IS da ke Syria da Iraq.

Somalia na fama da fadace-fadace na cikin gida, da cin hanci da rashawa da kuma hare-haren kungiyar Al Shabaab.