Manoma na bukatar tallafin noman rani

Manomi
Image caption Manoman na son inganta noman rani ba na damuna ka dai ba.

A Najeriya, wasu kananan manoma na ci gaba da kukan rashin kayan aiki, musamman ma na noman rani, kuma suna dakon irin daukin da za su samu daga gwamnatin kasar, ganin ikirarin da ta yi na inganta harkar noma.

A baya-bayan nan ma masu ruwa da tsaki kan al'amuran noma suka kamala wani taron koli da ake yi duk shekara a Kano domin lalubo hanyoyi inganta aikin noma a kasar.

Batun Iri na zamani da idan an shuka ya ke fitowa da wuri, wani babban kalubale ne ga kananan manoma da shi ma suke bukatar tallafin shi.

Wani Manomi Malam Abdullahi Ado, ya shaidawa BBC cewa babbar matsalar da suke fuskanta a halin yanzu ita ce ta yadda za su ci gaba da yin Noma ba lallai sai lokacin damuna ba.

Ma'ana su na bukatar tallafin da za su bunkasa noman rani da shi, dan hakan ne Malam Abdullahi ya roni gwamnatoci da su kawo musu dauki musamman ta hanyar gina musu rijiyar burtsatsai dan yin ban ruwa da shi a lokacin noman rani.

Haka kuma batun samun Taki a saukaka na daga cikin matsalolin da suke janyo koma baya ga noman da su ke yi, da kuma rashin wadatattun injinan ban ruwa na zamani.