Assad ka farka daga barci-Amurka

Assad ya ce za a iya magance rikicin kasar da karfin soji.

Asalin hoton, bbc

Bayanan hoto,

Assad ya ce za a iya magance rikicin kasar da karfin soji.

Amurka ta ce Shugaban Syria Bashar Al Assad na yaudarar kansa idan ya tsaya tunanin cewa za a iya magance rikicin kasar da karfin soji.

A wata hirar da aka yada ta kafafen yada Labarai, jiya Juma'a, shugaba Assad ya sha alwashin ci daga da gwabza fada har sai baki dayan Syria ta koma karkashin ikonsa.

Sai dai Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya ce babu abin da aniyar shugaba Assad za ta haifar face zubar da jinin al'uma.

A halin da ake ciki dai shugabannin manyan kasashen duniya da ke wani taro a Munich sun cimma wata yarjejeniyar da za ta taimaka wajen kawo karshen fadan da ake gwabzawa a kasar a cikin makon guda, kodayake 'yan tawaye sun ce ba za su mika makamansu ba sai Rasha ta daina yi musu ruwan boma-bomai.

Haka kuma suna bukatar lallai sai an tabbatar musu cewa za a fige shugaba Bashar Al Assad din daga kan karagar mulki.