Ana zaben shugaban kasa a C.A.R.

Hakkin mallakar hoto

Jama'a a jamhuriyar Afirka ta tsakiya suna kada kuri'a domin zaben sabon shugaban kasa a zagaye na biyu na zaben wanda ake fafatawa tsakanin tsohon Firaminista Faustin Touadera da kuma Anicet Dologuele.

Haka kuma ana zaben sabbin yan majalisar dokoki sakamakon soke zaben da aka a yi a watan Disamba saboda wasu kurakurai.

Dubban sojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suna sintiri a kan tituna domin bada cikakkiyar kariya ga zaben.

Ana fatan zaben zai kawo karshen rikicin kabilanci da na addini wanda ya biyo bayan hambarar da shugaban kasar Francois Bozize da kungiyar adawa wadda galibinta musulmi ne suka yi shekaru uku da suka wuce.