Paparoma John Paul ya yi mu'amala da matar aure

Hakkin mallakar hoto Photograph provided by Bill and Jadwiga Smith
Image caption Paparoma John Paul II da Ms Tymieniecka sun sha kadaicewa.

Daruruwan wasikun da BBC ta gani sun nuna cewa Paparoma John Paul II ya kwashe sama da shekarar 30 yana mu'amala ta kut-da-kut da wata matar aure.

An ajiye wasikun, wadanda aka aikewa Anna-Teresa Tymieniecka, 'yar asalin kasar Poland amma haifaffiyar Amurka, a dakin karatu na Poland domin kada mutane su gani.Wasikun sun nuna wata rayuwa ta daban da Paparoman, wanda ya mutu a shekarar 2005, ya yi sabanin ta rashin aure.

Sai dai babu wata shaida da ta nuna cewa Paparoman ya sadu da matar.

Paparoma John Paul II da Ms Tymieniecka sun fara mu'amala ta kut-da-kut ne a shekarar 1973 a lokacin da Ms Tymieniecka ta tuntube shi a lokacin shi ne Archibishop na Krakow, a kan wani littafi da ya rubuta kan falsafa.

A wancan lokacin, Paparoman, mai shekara 50, ya tafi Poland ne daga Amurka domin tattauna wa a kan littafin nasa.

Bayan ziyarar ne, sai mutanen biyu suka rika musayar wasiku.

Ms Tymieniecka ya kai ziyara a Vatican

Da farko dai, wasikun da Paparoman yake aike mata basu da kalamai na soyayya, amma daga bisani ya rika aike mata da kalaman soyayya ta kut-da-kut.

Paparoma John Paul II da Ms Tymieniecka sun yi aiki sosai a kan yadda za a sake wallafa littafinsa, mai suna, "The Acting Person."

Sun gana sau da dama - wasu lokutan ma sun rika bai wa juna kyautuka a asirce, yayin da a wasu lokutan suke kadaicewa.

A shekarar 1974, Paparoma John Paul II ya rubuta mata wasika inda ya shaida mata cewa yana sake karanta wasikunta guda hudu da ta rubuta masa a cikin wata daya, wadanda ya ce "suna da matukar ma'ana, sannan akwai zantuka da ke nuna alakar kut-da-kut a cikinsu".

Wasu hotunansu, wadanda ba a taba nuna wa jama'a ba, sun nuna yadda Paparoma ke shakatawa.

Ya gayyaci Ms Tymieniecka ta taya shi zuwa wajen motsa jiki da kuma yin wasan zamiyar-kankara - hasalima ta taba raka shi wajen wata ziyara da tawagarsa ta kai a wani waje.

Kazalika, hotunan sun nuna wata ziyara da ta kai masa a fadar Vatican.