Boutros Boutros-Ghali ya mutu.

Image caption Boutros Ghali ne mutum na farko da ya zama Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya daga kasashen Larabawa.

Majalisar dinkin duniya ta ce tsohon Sakatare Janar dinta, Boutros Boutros-Ghali, ya mutu yana da shekara 93 a duniya.

Shugaban kwamitin tsaro na majaliasar Rafael Dario Ramirez Carreno ya tabbatar da mutuwar Ghali.

Ghali, dan kasar Masar ne, kuma shi ne mutum na farko da ya fara zama Sakatare Janar na Majalisar daga kasashen Larabawa.

Ya zama Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya a shekarar 1992, inda ya yi wa'adi daya na shekara biyar.

'Yan kwamitin tsaro na majalisar sun yi shiru na minta daya domin nuna girmamawa ga tsohon Sakatare Janar na majaliasar ta dinkin duniya.