Yunkurin rage faduwar farashin man fetur

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sai dai kasar Iran ta ce za ta kara yawan man da take samarwa.

Hudu daga cikin manyan kasashen da ke fitar da man fetur sun amince su rage yawan man da suke hakowa da zummar dakatar da faduwar da farashinsa ke yi.

Kasashen Rasha da Saudiyya da Qatar da kuma Venezuela sun ce za su ci gaba da hako adadin man da suka hako a watan Janairu idan har sauran kasashen da ke kungiyar masu arzikin man suka amince da irin wannan mataki.

Sai dai tuni kasar Iran ta bayyana cewa za ta kara yawan man da take fitarwa bayan takunkumin da aka cire mata a watan jiya.

Farashin man fetur ya sake faduwa bayan wadannan kasashe sun bayyana manufarsu.