Nigeria: Majalisa ta ki yarda da karin kudin wuta

Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption Karin kudin wutar ya janyo zanga-zanga a Nigeria

Majalisar dattawan Najeriya ta umarci kamfanoni rarraba wutar lantarki na kasar da su cire karin kashi 45% da suka yi kan farashin wutar lantarki a kasar.

A yayin wani zama da ta yi ranar Talata, majalisar ta umarci kwamitinta na harkokin kwadago da ya kira wani taron jin koken jama'a na kasa baki daya domin sake yin nazari kan wannan batun, tare da duk masu ruwa da tsaki a sha'anin samar da hasken wutar lantarki.

A farkon wannan watan ne dai kamfanonin suka sanar da yin karin kudin wutar, abin ya sa kungiyoyin kwadago suka yi zanga-zangar kasa baki daya, domin nuna adawa da karin.

Senata Sulaiman Nazif shi ne shugaban kwamitin harkokin kwadago na majalisar dattawan, kuma ya yi wa Haruna Shehu Tangaza karin bayani:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti