Kotu ta yi watsi da bukatar Shugaba Sall

Hakkin mallakar hoto
Image caption Macky Sall ya so ya sauka daga mulki kafin cikar wa'adinsa.

Shugaban Senegal Macky Sall ya ce zai cigaba da zama a ofis har zuwa karshen shekarar 2019, bayan da kotun kolin kasar ta yi watsi da bukatarsa na rage wa'adin mulkin shugaban kasa daga shekara bakwai zuwa shekara biyar.

A wani jawabin da ya yi -- wanda kuma aka watsa a gidan Talabijin din kasar -- Mr Sall ya ce zai sa a gudanar da kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a a mako mai zuwa a kan batun.

A lokacin yakin neman zabensa a shekarar da ta gabata, Shugaba Sall ya dauki alkawarin rage wa'adin mulkin shugaban kasa.

Shugabannin kasashen Afirka da dama dai da suka hada da shugabannin Algeria da Angola da Chadi da Djibouti da kuma Uganda sun yi sauya tsarin mulkin kasar domin ci gaba da mulki.