Apple zai kalubalanci kotun Amurka

Kamfanin Apple ya ce zai kalubalanci wata kotun California, wacce ta bayar da umarni a yi kutse cikin wayar daya daga cikin mutanen da suka kai hare-haren San Bernadino wacce ke kulle da nufin taimaka wa hukumomi a binciken da suke gudanarwa.

A wata sanarwa da ya fitar, shugaban kamfanin na Apple, Tim Cook, ya ce idan har ana so ya yi biyayya ga umarnin kotun, to dole ne Apple ya samar da wata manhaja wacce za ta iya bude duk wayoyin da kamfanin ya kera .

Ya yi gargadin cewa hakan zai yi barazana ga sirrin masu mu'amala da wayoyin na Apple.

Syed Rizwan Farook da matarsa sun kashe mutum 14, kana suka jikkata mutum 22 a harin da suka kai a watan Disambar da ya wuce.

Ga rahoton da Ahmad Abba Abdullahi ya hada mana

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti