Sojojin Nigeria sun lalata sansanonin Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu farern hula hudu sun samu raunuka a lokacin farmakin

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta shiga dajin Alagarno tare da lalata wasu sansanonin da ta kira na 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Haka kuma rundunar ta ce wasu sojojinta uku sun samu raunuka a wani artabu da suka yi da 'yan kungiyar a ranar Talata.

Sojojin sun kwato jakai da dawakai da kayan abinci da wasu muggan makamai a sansanonin Boko haram din da ke dajin Alagarno da kuma Sambisa.

Sanarwar da rundunar ta fitar dauke da sa hanun kakakinsa Kanar Sani Usman Kukasheka ta ce, sojoji sun kashe 'yan Boko Haram hudu tare da raunata wasu da dama.

Wasu rahotanni dai sun ce har yanzu kungiyar ta Boko Haram na rike da wasu yankuna a wasu kananan hukumomi biyu a jihar ta Borno da ke arewa-maso-gabashin Najeriya.